Shin wai mine ne Ma'anar hak'a Bisharat?


Tambaya ce mai fuska biyu:
  1. Dommi ake buk'atar tsira fagen hazak'ar kimiya da sadarwa da kuma kyautata halin rayuwa ta fannin amfani da halsunan mama?
  2. Mine ne ma'anar kiran wannan yanar da "Bisharat"?

Amsa ga tambaya ta farko, ana iya samun ta ne a gaba, cikin wannan shafin; amsa ta biyu kuwa ana ambatar ta ne kawai a nan.

Ga albarkacin ilimin na'urar zamani, halayen al'amuran duniya na cudayyar jama'a, sai ci gaba da tasowa suke yi da sauri. Amma duk da haka, a fad'in Afirka da sauran wurare na kudu a bisa doron duniya, akwai k'arancin albarkatun na'urar zamani wad'anda za'a fuskanci hanyoyin labarai da sadarwa na zamani da su (kuma ga buk'atu iri-iri na sahun gaba sun fuskanto a gaggauce).

Ga halin haka kuwa, hanyoyin dacewa da dama sukan iya b'acewa in ba'a d'auki wasu matakai na aikata abubuwan da wuri ba. Bayan dogon nazari bisa ga dukan al 'amuran nan ne wasu ma'aikata da kungiyoyi masu zaman kansu, suke aiki domin su taimaki Afirka ta fannin sababbin hanyoyin labarai da sadarwa na zamani, ta a maido hankali wajen sawa a gane da yadda hanyoyin nan suke, da kuma yadda ake iya cin moriyarsu a aikace.

Ko da yake kad'an ne ma daga hanyoyin yanar na'urar, wad'anda suke d'an wayar da kai bisa ga mahimmancin abinda ake nufi da kuma abinda yanar take k'unshe da shi.

Halshen mama, bayan yana d'aya daga cikin abubuwa masu mahimmancin da za'a ba k'arfi ta fannin aiwata hanyoyin labarai da sadarwa na zamani, yana kuma d'aya daga cikin shikashiken da za'a bi a k'irk'iro abinda yanar na'ura mai k'wak'walwa zata k'unsa kuma domin a ciyo gurin masu bid'a da bincike daga yanar. Amma a tuna da halsunan Afirka basu samu sa'ar a aikata su ba, ta yadda za'a yi amfani da su ga na'ura mai k'wak'walwa ko a bisa yanar duniya gaba d'aya ta sadarwa. Haka ma sauran halsunan duniya suke a cikin wannan matsayin.

Rishin tsara sharhi mai daidaita yadda ake rubuta bak'ak'e na halsunan Afirka da sauran halsuna na duniya, yake kawo mishkila cikin aikin k'irk'iro na'ura mai iya karanta bakaken Afirka da sauran kasashe wadanda bakakensu daban ne da na turai.

Kenan dai matsalar dai ta shafi fannin lura da abinda yake wakana a halin rayuwa ta yanzu, hanyar sadarwa da albarkatu masu bada karfin aiwata aikin, amma ba matsalar fusa'ar tsara yin aikin ce ba.

A takaice, ga abinda ake buk'ata:

  • a ambaci wannan mishkilar a kowane taro na canza miyau tare da magabatan jagorar siyasar hak'a ilimin na'ura mai k'wak'walwa da kuma mutane masu hannu da shuni.
  • a k'arfafa huld'a tsakanin ma'aikata masu kyautata ci gaban halsunan Afirka da na sauran k'asashen da
  • ba na turai ba, da kuma hanyoyin labarai da sadarwa na zamani,
  • sak'a huld'a tsakanin ma'aikata masu aikin ci gaban al umma (makarantun yak'i da jahilci, k'ungiyoyi masu zaman kansu da sauransu...) da kuma mutanen da suke bincike na aikatawar hanyoyin labarai da sadarwa na zamani, dangance da matsalolin talauci, da dubunnan mutane suke fuskanta a halin yau.

Mai fasartawa Mallam Usman Nayaya Abubakar.