Shin wai mine ne Ma'anar haƙa Bisharat?


Tambaya ce mai fuska biyu:
  1. Dommi ake buƙatar tsira fagen hazaƙar kimiya da sadarwa da kuma kyautata halin rayuwa ta fannin amfani da halsunan mama?
  2. Mine ne ma'anar kiran wannan yanar da "Bisharat"?

Amsa ga tambaya ta farko, ana iya samun ta ne a gaba, cikin wannan shafin; amsa ta biyu kuwa ana ambatar ta ne kawai a nan.

Ga albarkacin ilimin na'urar zamani, halayen al'amuran duniya na cudayyar jama'a, sai ci gaba da tasowa suke yi da sauri. Amma duk da haka, a faɗin Afirka da sauran wurare na kudu a bisa doron duniya, akwai ƙarancin albarkatun na'urar zamani waɗanda za'a fuskanci hanyoyin labarai da sadarwa na zamani da su (kuma ga buƙatu iri-iri na sahun gaba sun fuskanto a gaggauce).

Ga halin haka kuwa, hanyoyin dacewa da dama sukan iya ɓacewa in ba'a ɗauki wasu matakai na aikata abubuwan da wuri ba. Bayan dogon nazari bisa ga dukan al 'amuran nan ne wasu ma'aikata da kungiyoyi masu zaman kansu, suke aiki domin su taimaki Afirka ta fannin sababbin hanyoyin labarai da sadarwa na zamani, ta a maido hankali wajen sawa a gane da yadda hanyoyin nan suke, da kuma yadda ake iya cin moriyarsu a aikace.

Ko da yake kaɗan ne ma daga hanyoyin yanar na'urar, waɗanda suke ɗan wayar da kai bisa ga mahimmancin abinda ake nufi da kuma abinda yanar take ƙunshe da shi.

Halshen mama, bayan yana ɗaya daga cikin abubuwa masu mahimmancin da za'a ba ƙarfi ta fannin aiwata hanyoyin labarai da sadarwa na zamani, yana kuma ɗaya daga cikin shikashiken da za'a bi a ƙirƙiro abinda yanar na'ura mai ƙwaƙwalwa zata ƙunsa kuma domin a ciyo gurin masu biɗa da bincike daga yanar. Amma a tuna da halsunan Afirka basu samu sa'ar a aikata su ba, ta yadda za'a yi amfani da su ga na'ura mai ƙwaƙwalwa ko a bisa yanar duniya gaba ɗaya ta sadarwa. Haka ma sauran halsunan duniya suke a cikin wannan matsayin.

Rishin tsara sharhi mai daidaita yadda ake rubuta baƙaƙe na halsunan Afirka da sauran halsuna na duniya, yake kawo mishkila cikin aikin ƙirƙiro na'ura mai iya karanta bakaken Afirka da sauran kasashe wadanda bakakensu daban ne da na turai.

Kenan dai matsalar dai ta shafi fannin lura da abinda yake wakana a halin rayuwa ta yanzu, hanyar sadarwa da albarkatu masu bada karfin aiwata aikin, amma ba matsalar fusa'ar tsara yin aikin ce ba.

A takaice, ga abinda ake buƙata:

  • a ambaci wannan mishkilar a kowane taro na canza miyau tare da magabatan jagorar siyasar haƙa ilimin na'ura mai ƙwaƙwalwa da kuma mutane masu hannu da shuni.
  • a ƙarfafa hulɗa tsakanin ma'aikata masu kyautata ci gaban halsunan Afirka da na sauran ƙasashen da
  • ba na turai ba, da kuma hanyoyin labarai da sadarwa na zamani,
  • saƙa hulɗa tsakanin ma'aikata masu aikin ci gaban al umma (makarantun yaƙi da jahilci, ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauransu...) da kuma mutanen da suke bincike na aikatawar hanyoyin labarai da sadarwa na zamani, dangance da matsalolin talauci, da dubunnan mutane suke fuskanta a halin yau.

Mai fasartawa Mallam Usman Nayaya Abubakar.