Shin, wai mine ne wannan sunan?


A sunanta mai matsayin tsira harkokin da suka shafi halsunan mama, da hanyoyin labarai da sadarwa na zamani da kuma bunk'asar rayuwar al ummar karkara da take sawaya a gaggauce, ana iya fahimtar sautin sunan Bisharat ta hanya ukku:

Da farko dai Bisharat bata da dangantaka tsaye sak da addinin Baha'i (ko kuma da wani addini daban), amma tsirawar yanar da aka yi, tana samun gamsuwa ne daga darussan baha'i, masamman ma a fuska biyu (ta a samu tsayayyen yare a cikin duniya wanda za'a yi amfanin sadarwa tsakanin bil adama, da kuma ganowar mahimmancin halsunan mama). D'aya daga cikin sak'on darussan baha'i, wanda yake bada k'arfin mahimmancin amfani da wani zab'ab'b'en yare "gama duniya" an yi mishi lak'anin "Bishárát."

Wannan tsirawar wadda take k'unshe da sunan Bisharat, ta samu tsinkaye ne daga mahimmancin a zab'i kuma a yi amfani da d'aya daga cikin halsunan duniya ta hanyar sadarwar cikin fahimtar juna, tana yiwuwa ta bada k'arfin cimma gurin nan na tsaida yaren "gama duniya".

Na biyu, kalmar bisharat, da ma'anar "albishir" ko "labari mai armashi", ta samu ne daga bak'ak'en larabci ب ش ر (ba - shin - ra), wa’danda suke iya nufin "rayuwar bil adama", ko kuma nufin k'arfafa dank'on zumunta tsakanin mutane tare da al adunsu ta hanyar sababbin fusa'o'in zamani na ci gaba da bunk'asa.

Hanya ta ukku a kan gaskiya, wasa ne na kalmomi tsakanin larabci da turanci. A cikin aikin ci gaba da bunk'asa, akwai adon magana iri-iri game da "grassroots" kamar "grassroots initiatives" a misalce. In aka maida hankali wajen Afirka, kamar "bush" a turance ko daji a hausance, tana kasancewa ne ko da yaushe. "Bush" ko daji, na ambatar mahalli inda aka hi amfani da illahirin halsunan Afirka. Da tsara tattalin ci gaba da bunk'asa, da kuma ba halsuna da al’adun galgajiya ladabi da matsiyi na gari, ana iya lak'antar tattalin karkara da "bushroot" a turance ko kyautata halin rayuwa tun daga tushe.


Mai fasartawa Mallam Usman Nayaya Abubakar.