Shin, wai mine ne wannan sunan?


A sunanta mai matsayin tsira harkokin da suka shafi halsunan mama, da hanyoyin labarai da sadarwa na zamani da kuma bunƙasar rayuwar al ummar karkara da take sawaya a gaggauce, ana iya fahimtar sautin sunan Bisharat ta hanya ukku:

Da farko dai Bisharat bata da dangantaka tsaye sak da addinin Baha'i (ko kuma da wani addini daban), amma tsirawar yanar da aka yi, tana samun gamsuwa ne daga darussan baha'i, masamman ma a fuska biyu (ta a samu tsayayyen yare a cikin duniya wanda za'a yi amfanin sadarwa tsakanin bil adama, da kuma ganowar mahimmancin halsunan mama). Ɗaya daga cikin saƙon darussan baha'i, wanda yake bada ƙarfin mahimmancin amfani da wani zaɓaɓɓen yare "gama duniya" an yi mishi laƙanin "Bisharat."

Wannan tsirawar wadda take ƙunshe da sunan Bisharat, ta samu tsinkaye ne daga mahimmancin a zaɓi kuma a yi amfani da ɗaya daga cikin halsunan duniya ta hanyar sadarwar cikin fahimtar juna, tana yiwuwa ta bada ƙarfin cimma gurin nan na tsaida yaren "gama duniya".

Na biyu, kalmar bisharat, da ma'anar "albishir" ko "labari mai armashi", ta samu ne daga baƙaƙen larabci ب ش ر (ba - shin - ra), waɗanda suke iya nufin "rayuwar bil adama", ko kuma nufin ƙarfafa danƙon zumunta tsakanin mutane tare da al adunsu ta hanyar sababbin fusa'o'in zamani na ci gaba da bunƙasa.

Hanya ta ukku a kan gaskiya, wasa ne na kalmomi tsakanin larabci da turanci. A cikin aikin ci gaba da bunƙasa, akwai adon magana iri-iri game da "grassroots" kamar "grassroots initiatives" a misalce. In aka maida hankali wajen Afirka, kamar "bush" a turance ko daji a hausance, tana kasancewa ne ko da yaushe. "Bush" ko daji, na ambatar mahalli inda aka hi amfani da illahirin halsunan Afirka. Da tsara tattalin ci gaba da bunƙasa, da kuma ba halsuna da al'adun galgajiya ladabi da matsiyi na gari, ana iya laƙantar tattalin karkara da "bushroot" a turance ko kyautata halin rayuwa tun daga tushe.


Mai fasartawa Mallam Usman Nayaya Abubakar.